′Yan Haiti na gudanar da zaben gama gari | NRS-Import | DW | 20.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

'Yan Haiti na gudanar da zaben gama gari

Soke sakamakon zaben watan Oktoban 2015 da hukumar zaben Haiti ta yi ne ya sa aka sake shirya sabon zaben shugaban kasa da na wasu kujeru na majalisun dokoki da na dattawan kasar.

'Yan Haiti miliyan shida da dubu 200 da suka cancanta na kada kuri'a da nufin zaben sabon shugaban kasa da 'yan majalisar wakilai da na dattawa, lamarin da zai bai wa kasar damar komawa kan turba madaidaiciya bayan rikicin siyasa da ta yi fama da shi. 'Yan takara 27 ne ke zawarcin kujera mai daraja ta shugabancin kasa, baya ga kujeru 27 na wakilai da za a subunta da kuma 16 na dattawa.

Aringizon kuri'u da yunkuri na murdiya ne suka sa hukumar zaben Haiti soke sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Oktoban 2015. Kanfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewar 'yan kasar da suka je runfunar zabe ba su taka kara sun karya ba. Wannan ba ya rasa naba da mawuyacin hali rayuwa na rashin ruwa mai tsafta da na sawa a bakin salati da suke fuskanta bayan mahaukaciyar guguwa da ta ratsa kasar.Idan ba dan takarar da ya sami gangarumin rinjaye tun a zagayen farko, za a fuskanci jinkiri wajen mika mulki ga zababben shugaban kasa kafin karshen watan Janairu na shekara mai kamawa.