´Yan gudun hijirar Afirka fiye da 64 sun nitse a tekun Aden | Labarai | DW | 23.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

´Yan gudun hijirar Afirka fiye da 64 sun nitse a tekun Aden

Aƙalla ´yan Afirka 64 dukkansu ´yan gudun hijira sun nitse a kudu maso gabashin gaɓar tekun Yemen lokacin da suke ƙoƙarin tsallake tekun Aden daga Somalia zuwa kasar ta Yemen. Kamfanin dillancin labarun ƙasar wato Saba ya ce daga cikin waɗanɗa suka rasu har da yara 3. Mutane 25 sun tsallake rijiya da baya lokacin da kwale-kwalen da ´yan gudun hijirar ke ciki ya nitse sakamakon lodi fiye da kima. Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi ƙiyasin cewa a wannan shekara sama da ´yan gudun hijira dubu 20 daga Somalia suka tsallake tekun Aden.