1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijirar Afirka a Italiya

April 30, 2010

An zargi Italiya da keta haƙin 'yan gudun hijirar Afirka

https://p.dw.com/p/NB7A
Hoto: AP

Bari mu fara da jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta rawaito kwamitin yaƙi da cin zarafin Bil Adama na majalisar ƙasashen Turai yana zargin ƙasar Italiya da keta haƙin Bil Adama dangane da matakan da take ɗauka kan 'yan gudun hijirar Afirka a tekun Bahar Rum, inda take mayar da su ƙasashen Aljeriya da Libya. A binciken da yayi a watanin Mayu da Yuni na shekarar 2009, kwamitin ya gano cewa gwamnatin Italiya ta keta dokar korar baƙin haure daga ƙasar domin tana mayar da 'yan gudun hijirar ne ƙasashen da ake iya cin zarafinsu. To sai dai gwamnatin Italiya ta yi watsi da wannan zargin tana mai cewa ana zaunar da 'yan gudun hijiran a ruwayen ƙasa da ƙasa dake gaɓar tekun Libya da Aljeriya kafin a mayar da su ƙasashensu na asali.

Afrikaner mit deutscher Fahne
Hoto: picture-alliance / dpa

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung ta mayar da hankalinta akan hukuncin da hukumar gudanarwar birnin Berlin ta yanke inda ta hana a mayar da wata mata 'yar Togo da ɗanta mai shekaru 10 gida. Ta ce yanzu Ginette da Gergi Liebl suna da izinin ci-gaba da zama a nan Jamus sakamakon matakin gaggawa da hukumar ta Berlin ta ɗauka na mayar da batun 'yan Togon ƙarƙashinta daga hukumar jihar Bavariya. Da farko dai da a wannan Alhamis da ta gabata ya kamata a tasa ƙeyarsu zuwa Togo. Tun a bara ne aka koma da mijin Ginett wato Gerson gida bayan ya shafe shekaru 18 yana gwagwarmaya domin tabbatar da cewa shi Bajamushe ne. Wannan batu dai ya kai ga kotun kare kundin tsarin mulki kuma ya ɗauki hankalin jama'a saboda rashin wani tambari daga zamanin sarkin sarakunan Jamus da zai tabbatar da sahihancin aure tsakanin kakansa Bajamushe da wata 'yar Togo.

WM Städte und Stadien der Fußball WM in Südafrika Bloemfontein
Hoto: AP

Ita kuwa a sharhinta jaridar General Anzeiger ta taɓo wani zaman muhauwara ne da aka yi a nan Bonn ƙarƙashin taken: Wane alfanu Afirka Ta Kudu za ta samu sakamakon karɓar baƙwancin gasar cin kofin ƙwallon ƙafa na duniya? Masana tattalin arziki da wasan ƙwallon ƙafa sun daɗe suna saka ayar tambaya kan shin mai zai saura ga Afirka ta Kudu bayan kwanaki 30 na wasannan ƙwallon ƙafar duniya? Shin za a samu ci-gaba mai ɗorewa sakamakon gasar kofin duniyar? Wane fata 'yan Afirka ta Kudu ke yi? Shin ko ya ma dace a bawa wata ƙasa mai tasowa nauyin shirya gasar? A ƙarshe dai masana harkokin yau da kullum na Afirka sun ce gasar ƙwallon ƙafa ba za ta kawo wani sauyi na a zo a gani a ƙasar ba domin ga FIFA wannan wasan motsa jiki ne kawai. Kuma hasali ita FIFA ta fi mayar da hankali ne kan ribar da za ta samu amma ba wani aikin raya ƙasa ga Afirka ba. Alƙalumman lissafi sun yi nuni da cewa Afirka Ta Kudu ta kashe Euro miliyan dubu 2.6 wajen gine-ginen hanyoyi da wuraren wasa, abin da ya haura yawan kuɗaɗen da ta kashe a ayyukan raya ƙasar musamman gina gidaje cikin shekaru 10 da suka wuce.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Umaru Aliyu