Yan gudun hijiran somalia na cikin halin ni yasu | Labarai | DW | 24.08.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan gudun hijiran somalia na cikin halin ni yasu

Kimanin yan gudun hijira dubu 140 yan kasar Somalia,dake jibge a sansaninsu dake arewacin Kenya n eke cigaba da kasancewa cikin halin kakanikayi na rayuwa,sakamakon rashin tallafin abinci daga kasashen ketare.kungiyar bada tallafin kasa da kasa ta CARE international ta sanar dacewa,hukumar kula day an gudun hijira ta mdd da kungiyar bada tallafi ta Amurka,sun rage yawan kudaden agaji da suke bawa sansanin yan gudun hijiran na garin Dadaab,da kashi 23 daga cikin 100.

Adangane da hakane kungiyar tace ,wannan hali ya jefa yan gudun hijiran somalian cikin hali matsananci na karancin rowan sha,da muhalli da harkokin ilimi,ayayinda ana saran Karin yan gudun hijira kimanin dubu 30 nanda karshen shekarar da muke ciki.Jamiin Care International Mohammed Qazilbash,y ace rage kudaden tallafawa yan gudun hijiran yazo adai dai da lokacin da rigingimu ke dada barkewa tsakanin gwamnatin riko,da hadin gwiwar kungiyoyin kotunan Islama,a hannu guda kuma da shugabannin hauloli na somalian.

 • Kwanan wata 24.08.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5o
 • Kwanan wata 24.08.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5o