1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijiran Siriya za su fiskanci karancin abinci

Muntaqa AhiwaDecember 1, 2014

Majalisar Dinkin Duniya ce ta sanar da wannan labarin, sakamakon rashin samun kudaden da aka yi alkawarin samar mata domin ta iya samar da abincin.

https://p.dw.com/p/1Dxpr
Welternährungsprogramm WFP Nahrung für Flüchtlinge
Hoto: WFP/Rein Skullerud

Wata cibiyar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Rome na kasar Italiya, ta ce 'yan gudun hijiran dake cikin kasashen Jordan da Lebanon da Turkiyya da Iraki da kuma Masar ne, zasu rasa agajin na abinci, muddin wadanda suka yi alkwarin samar da Euro miliyan 64 da ake bukata na wadata su da kayan abincin.

Wani babban daraktan samar da abincin na UN, Ertharin Cousin, ya shaidawa kamfanin dillacin labaran AFP na Faransa cewa wannan matsala za ta fi shafar lafiyar 'yan gudun hijira ne wadanda tuni ke cikin mawucin hali musamman kananan yara da a yanzu ko takalma basu dasu, wadanda kuwa ke fakewa da iyayen su cikin 'yan runfuna.