1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijiran Najeriya na bukatar yin zabe.

Ardo Abdullahi HazzadMarch 13, 2015

Daruruwan 'yan gudun hijiran da ke fake wa a jihar Bauchi, na kiran mahukunta da su taimaka masu su sami damar komawa gidajensu don taka rawa a zaben kasar da ke tafe.

https://p.dw.com/p/1EqKa
Flüchtlingslager Minawao in Kamerun
Hoto: DW/M.-E. Kindzeka

Dubban 'yan gudun hijran da su ka tsere daga jihohin Borno da Adamawa sakamakon rikicin Boko Haram da suka samun mafaka a jihar Bauchi, na jan hankalin gwamnatocinsu da su agaza musu da kudi ko motoci domin su koma jihohin na su don kada kuri'unsu a zaben shugaban kasa da ke tafe a kasar cikin makwanni biyu.

Akasarin ‘yan gudun hijiran dai sun fito ne daga garuruwan Gwoza da Baga na jihar Borno, sai kuma wasu daga Michika da Madagali da ke jihar Adamawa. Kamar yadda su ke bayani, za su fi son komawa garuruwan na su da suka tsallake sakamakon tashin hankalin don yin zabe kamar ko wane dan kasa.

‘Yan hijiran na Borno da ke Bauchi sun zarta dubu uku kamar yadda su ka shaidar, sai su ma daruruwa daga jihar Adamawa, babban kuma bukatarsu a yanzu, ita ce gwamnatocin jihohinsu su hada kai da gwamnatin jihar Bauchi domin sama masu mafita a wannan matsala da su ka sami kansu ciki.