1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan gudun hijira daga somaliya na kwarara zuwa Kenya

Zainab A MohammadOctober 6, 2006
https://p.dw.com/p/Bu5D

Sama da yan kasar Somalia dubu 2 sukayi gudun hijira daga matsugunnensu zuwa cikin Kenya takan iyaka ,cikin kwanaki 2 da suka gabata,ayayinda ake rade radin cewa mayakan kotunan islama sun garuruwan dake kwarin Juba,Kakakakin komissinar yan gudun hijira ta mdd Jennifer Pagonis ,wadda ta sanar da hakan ta bayyana cewa wannan kwararan yamn gudun hiran yazo ne adaidai lokacin da ake yayata cewa wasu mayakan dake da alaka da kotunan islaman Somalian sun kai somame garuwan dake kudancin Somalian.Tun daga farkon wannan shekara kawo yanzu dai,akwai yan gudun hijiran somaliyan kimanin dubu 30 da suka shiga garin Amuma dake Kenya ,domin neman mafaka.Tun bayan da gamayyar kotunan musulmin suka kwace birnin Mogadisho daga hannun shugabannin hauloli da Amurka ke marawa baya a watan yuni nedai,suka shiga cafke sauran garuruwan kudancin wannan kasa dake da yawan alumma milion 10.