1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sanyi ya takura wa 'yan gudun hijira a Jamus

January 18, 2017

Mafi akasarin 'yan gudun hijira da ke Jamus yanzu haka sun fito ne daga kasashen da ba matsanancin sanyin hunturu wanda ake fama da shi a kasar wannan lokacin. Wasu sun suna koka.

https://p.dw.com/p/2VysV
Deutschland Flüchtlinge in Berlin LaGeSo
Hoto: picture alliance/dpa/G. Fischer

Su dai wadannan Yan gudun hijiran sun baro kasashensu ne zuwa Jamus don neman mafaka sai dai yanayin zamantakewa ya banabanta da kasashen su na asali musamman ma matsanancin sanyin hunturu da ake fama da shi a Jamus a wannan lokacin.  Da yawan su sai da suka zo Jamus suka ga Yadda dusar kankara ke zuba musamman ma wadanda suka fito daga Afirika.

Deutschland Flüchtlinge in Passau
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Weigel

Karam likitan dabobine dan asalin Siriya wanda ya sami mafaka a Jamus ya bayyana halin da suke ciki a wanan sanyin hunturu.

"Babbar matsalar mu ita ce tsananin sanyi da ake fama da shi yanzu da rashin isasun na'urorin zafafa dakuna. Ya zama dole mutum ya kasance yana sanye da tufafi biyu zuwa uku don ya kara yi ma kansa maganin sanyi."

Shi ma Abdulhadi yana samun mafaka ne a Jamus, shi din ma daga Siriya yake, yana mai cewa.

"Yanzu haka karfin sanyi ya yi tsanani don ya kai har kasa da sifili, a nan sansanin komai ma sai a hankali inda a tanti guda sai ka sami mutum sama da hamshin"

Wani dan Afirika wanda bai amince a bayyana sunan sa ba, yana daya daga cikin dubban mutanen.

"Ni a gida ba ni da wata matsala don na'urar zafafa dakinmu tana aiki sosai, matsala ta a wannan hunturun dai ita ce kai da kawowa cikin sanyi don ya zama dole mutum ya fita, da kuma matsalar rashin abin hawa."

Sanyin hunturu a Turai shi ne abin nan da Hausawa ke ma kirari da " Soja marmari daga nesa" wato ganin shi a nesa ya fi ka kusance shi.