1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira a Pakistan

Tijani LawalOctober 20, 2009

A halin yanzu haka ƙasar Pakistan na fama da dubban ɗaruruwan 'yan gudun hijira da suka tagayyara a cikin gida

https://p.dw.com/p/KBAI
'Yan gudun hijira a WaziristanHoto: AP

Ko shakka babu, al'umar kudancin Waziristan na ƙasar Pakistan sun samu kansu cikin wani wadi na tsaka mai wuya sakamakon hare-haren da dakarun sojin kasar ke kaiwa a wannan yanki. Hakan ya samu ne bayan da aka fuskanci karuwar yan gudun hijra sakamakon harin da dakaru suka kai a yankin arewa ymaso ammacin kasar ta Pakistan. Wannan hali dai zai kara kazanta a wannan karon a lardunan kudancin Waziristan da kuma Swat.

Ko kafin ɓarkewar wannan faɗa, Majalisar Ɗinkin Duniya ta rubuta sunayen 'yan gudun hijra sama da dubu 80 daga kudancin Waziristan. Da yawa daga cikin 'yan gudun hijrar dai sun yi kaura ne zuwa gundumar Dera Ismail Khan. Manuel Bessler shi ne shugaban shugaban ofishin Majalisar Ɗinkin duniya da ke kula da aikin ba da agaji a birnin Islamabad:

"Akasarinsu suna raɓe wajen dangi. Akwai kuma wasu da ke zaune a wasu wurare daban. inji Manuel Bessler Ya ci gaba da cewa Saboda kasancewar Waziristan wuri ne da ke kan tsauni, da yawa daga cikinsu su kan bar gidajen su domin gudun sanyin hunturu inda suka ƙaura zuwa gidajensu na biyu da ke gangaren wannan lardi"

Sai dai kuma akwai wasu da har yanzu ke fuskantar matsalar rashin wurin barci. A baya ga haka ana fuskantar rashin takammamiyar gwamnati a yankunan masu tsaunuka da ke bakin iyakar kasar da Afganistan. An ƙiyasce cewa kimanin mutane ɗari biyar suka foto daga kudancin Waziristan kamar yadda Bessler ya nunar:

Yace muna sa ran samu ƙaruwar yawan yan gudun hijrar da dubu dari biyu da hamsin ko kuma fiye da haka. Hakan na nufin cewa za a bar kusan dubu dari biyu a baya. Anma kuma wajbi ne a yi la'akari da cewa hare-haren da sojoji ke kaiwa basu shafi baki dayan lardin Wazirista ba. Akwai wasu wurare dab ke ciki kwari da wannan faɗan bai shafa ba."

Ma'aikatan agajin dai na buƙatar ba da taimakon abinci ga 'yan gudun hijirar. A baya ga bukatar samar da ruwan sha, magunguna da tsabta . Akwai kuma buƙatar komawa da yara zuwa makaranta. A ko da yaushe dai Manuel Bessler kyautata fata ya ke game da samun isasshen kuɗin gudanar da aikin taimakon jinƙai. Bessler ya ƙara da cewa:

"A haƙiƙa a ko da yaushe ana fuskantar matsalar rashin kuɗi. A dai halin da ake ciki yanzu kashi 65 daga cikin ɗari na kuɗin da muke bukata ne kaɗai mu ke samu. Amma kuma akwai bukatar yin tanadi sosai dubi ga yiwuwar ci gaban wannan rikici da ake shafe watanni ana fuskanta a Waziristan. A sabo da haka mun kafa cibiyar ba da taimakon jinƙai a bakin ƙogín Indus na ɓangaren lardin Punjab, inda muka tanadi abinci magunguna, ruwan sha da kayan tsabtace kewaye da suka haɗa da kayan girki da guguna, domin ɗaukar matakin gaggawa saboda cewa tazarar kilomita biyu kaɗai ne ke tsakanin wannan wuri da inda ake rikicin."

Ga baki ɗaya an tabbatar da buƙatar kula da 'yan gudun hijira kimanin miliyan biyu da ɗigo bakwai na cikin gidan ƙasar ta Pakistan da suka fito daga lardin Swat da kuma lardunan da ke makwabtaka da shi. A lokaci lokaci dai an samu yan gudun hijira miliyan guda da suka koma yankunansu na asali. To sai dai kuma akwai buƙatar ci gaba da ba da taimako ga da yawa daga cikin waɗanda suka koma lardin Swat . A dai halin da ake ciki yanzu Majalisar Ɗinkin Duniya ba ta dakatar da aikinta na ba da taimakon jinƙai ba duk da harin da aka kai wa ofsihin shirin abincin duniya da ke birnin Islamabad.

Mawallafi: Halima Balaraba Abbas

Edita: Ahmad Tijani Lawal *