1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan fashin teku sun sako Jamusawa biyu

July 4, 2010

Kimanin mutane goma sha biyu ne aka sako ba tare da ƙwarzane ba

https://p.dw.com/p/OAXF
Wasu 'yan bindigan Naija-DeltaHoto: picture alliance / dpa

'Yan fashin teku a yankin Neija Delta - mai arzikin man fetur da ke tarayar Nijeriya sun sako wasu Jamusawa biyu ma'aikatan wani jirgin ruwar ɗaukar kaya da suka sace a Nijeriya.

Kakakin rundunar Sojin ruwan Najeriya Kwamandan David Nabaida ya shedawa kanfanin dillancin labaran AP cewar an kuma sako wasu ma'aikata 10 na jiragen ruwa da suma akayi garkuwa dasu da suka haɗa da Rashawa buyu.

A daren juma'a ne dai 'yan fashin suka haura jirgin mai ɗauke da tutar jamus da ake kira bbc Palonia a lokacin da yake yankin ruwan na Niger Delta.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Uamru Aliyu