Yan fashi sun kashe jamiin soja a Agadas din Niger | Labarai | DW | 11.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan fashi sun kashe jamiin soja a Agadas din Niger

Wani jamiin soji ya rigamu gidan gaskiya,kana an sace guda a garin agadas dake arewacin janhuriyar Niger,lokacin da wasu yan bindiga dadi suka afkawa wani ayarin motocin dake dauke da kayyayaki bisa ga rakiyan jamian sojin.Yankin dake kasancewa tsohon wurin hada hadan kasuwanci,mai tazarar km 1,700 arewacin fadar gwamnatin kasar dake Niamey,na mai zama cibiyar tashe tashen hankulan yan tuareg makiyaya a shekarun 1990,inda kawo yanzu ana cigaba da fama da matsalolin yan fashi da makamai.To sai dai kafofin yada labaru daga Niger din na nuni dacewa,wadanda suka aikata wannan taassar baki ne daga kasar Tchadi dake makwabtaka.Ayayinda a hannu guda kuma majiyar Niger din na taka tsantsan da bayyana kasar da suka fito.Masu kai harin dai sun afkawa motoci biyar ne dake cike da tabar sigari daga agadas din zuwa kasar Libya,wadda ke zamma cibiyar kasuwancin taba a wannan yanki.