Yan fashi sun kama wasu jirage ukku na ƙasar tailand | Labarai | DW | 20.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan fashi sun kama wasu jirage ukku na ƙasar tailand

Masu fashin jiragen ruwa a ƙasar Somaliya sun kama wasu jiragen kamun kiffi ukku na ƙasar tailan

default

wani mayaƙin ƙungiyar Al-Shabaab

Masu fashin jiragen ruwa a ƙasar somalia sun kame wasu jiragen ruwa ukku na kamun kiffi na ƙasar Tailan mita 1200 a gaɓar gabacin tekun somaliyar.

Sanarwa wace dakarun ruwa na ƙungiyar taraya turai ta bayyana, ta ce tun ranar lahadi aka kama jiragen dake dauke da masunta 77 dukaninsu yan kasar Tailan ,,kakakin rundunar John Harbour ya sheda cewa suna ci gaba da bincikke domin gano ind jiragen suke.

Sanan kuma wasu rahotanin daga Mogadiscio sun ce mutane biyar suka mutu yayin da wasu bakwai suka jikata a sakamakon barin wutar da ake da mayan makamai tsakanin dakarun gwamnatin da yan ƙungiyar alshabab masu kishin adinin islama.