1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan Djandjawid sun sake kai hari a Darfur

April 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuOY

Kakakin rundurar shiga tsakani, ta ƙungiyar tarayyar Afrika a yankin Darfur na ƙasar Sudan, ya bayyana cewar wasu mutane ɗauke da manyan rokoki,sun harbi jirgin rundar shiga tsakani,ta Afrika a yayin da ya ke ɗauke da mataimakin shugaban rundunar, a kan hanyar sa, ta zuwa Alfacher.

Saidai babu wanda ya ji rauni a sakamakon wannan hari.

A dalili da haka,an shirya taro tsakanin wakilan dakarun Afrika, da na ƙungiyar tawayen da ta rattaba hannu a kann yarjeniyar zaman lahia, da zumar dakatar da wannan aika-aika, wadda ke matsayin koma baya, ga yunƙurin Afrika, na tabbatar da tsaro a yankin Darfur.

Wannan saban hari ya wakana, jim kaɗan bayan da mayaƙan Janjawid, masu ɗaurin gidin gwamnatin Khartum, suka abkwa, al´ummomin wannan yanki,a jiya asabar.

A ƙalla mutane 43 su ka rasa rayuka a sakamakon harin, inji Ibrahim Ahmed Ibrahim wani shugaba ƙungiyar tawaye.