Yan Chechnya sun kashe sojojin Rasha | Labarai | DW | 25.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan Chechnya sun kashe sojojin Rasha

Chechnya/Killings

Sojjojin Rasha biyarne suku mutu wasu hudu kuma suka sami raunuka a hare hare daban daban da yan awaren Chechnya suka kai musu a lardin kudancin chechnya wanda yaki ya balbalta a karshen makon nan.

Wani jamiin gwamnatin Chechnyan wadda ke samun goyon bayan gwamnatin Rasha daya bukaci a boye sunansa ne ya shedawa kamfanin dillanci labarai na Associated Press.

Jamiin yace yan tawayen sun rinka kaiwa sojojin Rasha hare hare a wurare daban daban har sau goma sha daya.

A yanzu dai an shiga shekarata shida kenan da hadin gwiwar sojojin Rasha da jamian tsaron Chechnya suke ta fafatawa da yan awaren na chechnya wada da sukle neman ballewa daga Rasha,yakin da ya zamo na biyu tun alif dari tara da casain da hudu .

Koda kie hukumomin Rasha sukace alamura na komawa dai dai a wannan yanki amma kusan a kowaca rana sai an kashe ko jikkata walau sojan Rasha ko na yan tawayen.