1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

´Yan bindiga sun yi garkuwa da ma´aikatan wata kungiyar agaji

December 17, 2006
https://p.dw.com/p/BuXU
Wasu ´yan bindiga dadi sanye da kayan sojin Iraqi sun yi garkuwa da ma´aikata da dama daga ofishin kungiyar ba da agaji ta Red Crescent dake birnin Bagadaza. ´Yan sanda sun ce ´yan bindigan wadanda suka je ofishin a cikin motocin a kori kura sun yi awon gaba da ma´aikata maza ne kadai. Red Crescent wadda ta ke reshe na kungiyar agaji ta Red Cross ta na da ma´aikata kimanin dubu daya a fadin Iraqi baki daya. A kuma halin da ake ciki wani bam da aka dana a gefen hanya ya halaka sojojin Amirka 3 sannan ya jikata daya a arewacin birnin Bagadaza. Yawan sojin Amirka da aka kashe a wannan wata a Iraqi yanzu ya kai 57. Kasashen duniya dai sun yi marhabin da matakin da FM Nuri Al-Maliki ya dauka na sake shigar da tsofaffin sojin Iraqi karkashin tsohon shugaban kasa Saddam Hussein a cikin rundunar soji a wani mataki na dinke barakar dake tsakani.