´Yan bindiga sun yi garkuwa da ma´aikatan mai a Nijeriya | Labarai | DW | 02.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

´Yan bindiga sun yi garkuwa da ma´aikatan mai a Nijeriya

Wasu ´yan bindiga a cikin kayan jami´an tsaro sun yi awon gaba da baki 4 ma´aikatan mai a kudancin Nieriya, a daidai lokacin da wasu ´yan takife suka saki wasu bakin ma´aikatan mai 6 da aka yi garkuwa da su a ranar daya ga watan mayu. Kakakin kungiyar kwato ´yancin yankin Nijer Delta wato MEND a takaice ya ce an sako Italiyawa 4 da Ba-Amirke daya da kuma dan Kuratiya daya kuma yanzu haka an mika su ga hukumomin jihar Bayelsa dake kudancin Nijeriya. Ma´aikatar harkokin wajen Italiya ta tabbatar da sakin mutanen kuma yanzu haka suna hannun jami´an kamfanin da suke yima aiki wato Chevron.