1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun kashe mutane a Zamfara

April 20, 2018

Wasu 'yan bindiga a Najeriya, sun kashe mutane da dama a jihar Zamfara da ke yakin arewa maso yammacin kasar.

https://p.dw.com/p/2wPDW
DW - eco@africa: Nigerianische Farmer und der Klimawandel
Hoto: DW

Rahotannin da ke fitowa daga Najeriya, na cewa wasu ‘yan bindiga sun halaka mutane 27 a karamar hukumar Maru da ke jihar Zamfara da ke yakin arewacin kasar. Kashe-kashen dai sun faru ne lokacin da 'yan bindigar suka shiga kauyuka tare da buda wuta kan jama'a.

Shugaban karamar hukumar Maru Salisu Isa Dan Gulbi ya tabbatar da afkuwar lamarin. Shi ma wani ganau ya tabbatar wa wakilinmu Yusuf Ibrahim Jargaba cewar ya ga gawarwaki 27, kuma wasu motoci 2 na jami'an 'yan sanda na aikin kwashe gawarwaki. An dai yi kokarin jin ta bakin jami'an tsaro a jihar, sai dai ba a yi nasara ba.

Jihar ta Zamfara na daga cikin jihohin arewacin Najeriyar da ke fama da matsalar kashe-kashe da 'yan bindiga ke yi, da kuma ake matukar kokawa a kansa.