′Yan bindiga sun kai hari a wani gidan yari a Mali | Labarai | DW | 06.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan bindiga sun kai hari a wani gidan yari a Mali

Hukumomi a kasar Mali sun tabbatar da tserewar fursunoni da dama daga gidan yari biyo bayan wani hari da ake zargin 'yan ta'adda ne suka kai a garin Niono da ke tsakiyar kasar.

Babu tabbacin ko akwai wani dan kungiyar ta'adda da ke tsare a gidan yarin da ake tunanin 'yan uwansu suka kubutar, amma dai mai magana amadadin ma'aikar tsaron kasar Mali, Abdoulaye Sidibe ya ce sojoji sun yi nasarar maido da wasu fursunonin da suka tsere, kuma dakarunsu na ci gaba da nausawa dan ganin an kai ga cimma maharan.

A watan da ya gabata ma dai 'yan bindiga sun kaddamar da hari tare da fasa wani gidan yari a kudancin Mali, inda suka yi yunkurin kubutar da fursunoni biyu. A baya dai sojojin Faransa sun sha fatattakar 'yan tawayen arewacin Mali da ke zafafa kai hare-hare a sassa daban-daban na kasar.