′Yan bindiga sun harbe wani jigo a jam′iyyar adawa ta ANPP a Nijeriya | Labarai | DW | 07.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan bindiga sun harbe wani jigo a jam'iyyar adawa ta ANPP a Nijeriya

Mataimakin shugaban jam'iyyar ANPP a Nijeriya ya rasa ransa sakamakon harbin da wasu 'yan bindiga suka yi masa

default

Farmakin da jami'an tsaro suka kaiwa hedikwatar Boko Haram

Hukumomin tsaro da kuma manbobin jam'iyyar ANPP da ke mulki a jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin Nijeriya, sun tabbatar da cewar, wani harin da ba'a tantance wadanda suka kai ba, ya yi sanadiyyar mutuwar mataimakin shugaban jam'iyyar ANPP ta kasa a Nijeriya. Kakakin jam'iyyar ANPP ta kasa Emmanuel Eneukwu ya ce harin da aka kai a gidan Awana Ali Ngala da ke birnin Maiduguri ya yi sanadiyyar mutuwar sa da yammacin Larabar nan. Eneukwu ya kara da cewar, ana zargin mambobin kungiyar Boko haramun ne suka kaddamar da harin. Ko da shike jam'an 'yan sanda ma sun tabbatar da kissan, amma wani babban jami'in dan sandan daya bukaci a sakaya sunan sa ya ce wasu mutanen da ba'a san ko su wanene ba ne suka shiga gidan Ali Ngala suka harbe shi. Gabannin harin daya janyo mutuwar Ngala dai, wasu mutane dauke da bindigogi sun kaddamar da hari a gidan Ali Modu, shugaban Majalisar dokokin jihar ta Borno tare da kissan wani jami'in tsaro, kamar yadda 'yan sanda da kuma kakakin jam'iyyar ANPP suka tabbatar. Wannan dai na daga ciki jerin hare haren da ake kaiwa jami'an gwamnati da kuma 'yan sanda game masu unguwanni a jihar ta Borno.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Ahmad Tijani Lawal