’Yan bindiga na ci gaba da yin garkuwa da mutane a Iraqi. | Labarai | DW | 18.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

’Yan bindiga na ci gaba da yin garkuwa da mutane a Iraqi.

A ƙasar Iraqi, wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da ma’aikata 10, na wata masana’antar burodi da ke unguwar mabiya ɗariƙar shi’iti a birnin Bagadaza. Wannan kuwa ya biyo bayan wani harin bam da na rokoki ne da aka kai jiya a birnin, inda mutane kusan 40 suka rasa rayukansu.

Masharhanta na jiɓinta hare-haren ne da sabon shugaban ƙungiyar al-Qaeda a Iraqin, Abu Ayyub al-Masri, wanda ya lashi takobin ɗaukan fansa kan waɗanda ke da hannu a mutuwar tsohon shugaban ƙungiyar, Abu Musab al-Zarqawi, wanda ya ganu da ajalinsa, yayin da dakarun Amirka suka kai wa gidan da yake ciki hare-haren bamabamai da jiragen saman yaƙi, a ran 7 ga wannan watan.

’Yan yaƙin gwagwarmayar Iraqin dai sun iza wuta a hare-harensu ne, don ƙalubalantar wani ɗaukin da Firamiyan ƙasar, Nuri al-Maliki ya gabatar a makon da ya gabata, wai na tabbatad da tsaro a birnin na Bagadaza.