'Yan binda sun hallaka mutane uku a jihar Bayelsa
September 23, 2017'Yan bindigan dai da ba bayyana ko suwanene ba sun kai wa wani jirgin ruwa mai dauke da jami'an tsaro da kuma fararan hulla hari a yankin Ekebiri a cewar Asinim Butswat mai magana da yawun 'yan sandan jihar Bayelsa, wanda ya ce masu aikin ceto sun iso cikin gaggawa inda suka ceci rayuwar wani dan sanda, da kuma wasu membobin rundunar tsaro ta NSCDC guda hudu, sannan da wasu fararan hulla guda hudu.
Jami'an tsaron da hafaran hullan da ke tare da su, sun fuskanci kwanton bauna ne daga 'yan bindigar kusa da al'ummar Okoron yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa cibiyar mai ta Tebidaba mallakar kampanin Agip Oil na kasar ta Najeriya. Sai dai mazauna yankin sun ce an samu musayar wuta tsakanin jami'an tsaron da 'yan bindigan da ake zaton masu fashin jiragen ruwa ne.