′Yan awaren PPK sun dauki alhakin kai harin Santanbul | Labarai | DW | 11.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan awaren PPK sun dauki alhakin kai harin Santanbul

Kungiyar Kurdawa masu dauke da makamai a Turkiyya, ta dauki alhakin harin da aka kai da yammacin ranar Asabar a birnin Santanbul, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 38, tare da jikkata wasu mutanen 155.

Türkei Istanbul nach den Anschlägen (Reuters/O. Orsal)

Kungiyar PKK ta dauki alhakin harin Santanbul

Cikin wani sako da suka aike ta shafinsu na Twitter, kungiyar fafutukar samun 'yancin yankin Kurdawa da ke a matsayin kungiyar 'yan awaren jam'iyyar ma'aikata ta Kurdawan kasar wato PKK, sun ce su ne suka kai wadannan tagwayen hare-haren a kusa da filin wasa na Besiktas da ke tsakiyar birnin na Santanbul.

A cewar ministan cikin gidan kasar Suleyman Soylu adadin wadanda suka mutu ya karu ne cikin dare, inda cikin mutane 38 da suka mutu akwai 'yan sanda 30, sannan daga cikin wadanda suka jikkata 14 na cikin mawuyacin hali. Tuni dai hukumomin tsaron kasar suka cafke wasu mutane 13 da ake zargi da hannu cikin lamarin, tare da shan alwashin daukar fansa kan wadanda suka aikata wannan mummunan hari.