1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawar Syriya za su halarci sulhun Geneva

Kamaluddeen SaniMarch 7, 2016

A ranar Litinin din nan ce kakakin 'yan adawar kasar Syriya Riad Naasan Agha ya bayyana cewar sun cimma yarjejeniyar halartar taron sasantawar da Majalisar Dinkin Duniya ta ke shiga tsakani.

https://p.dw.com/p/1I8ff
Genf Friedensverhandlungen zu Krieg in Syrien - Riad Naasan Agha
Hoto: Getty Images/AFP/F. Coffrini

Mai Magana da yawun 'yan adawar ya ce bayan tuntubar juna da suka sha yi yanzu haka babban kwamitin koli na tattaunawar ya amince da ya yi tattaki zuwa birnin Geveva domin shiga tattaunawar da gwamnatin kasar Siriya da kuma masu shiga tsakani.

A ranar Juma'ar nan ce dai ake sa ran hallarar tawagar bangarorin biyu domin tinkarar magance matsalar yakin Syriyan.

Tun dai a ranar 27 ga watan Febarairu ne 'yan adawar suka yi shakulatin bangaro wajen bayyana domin tattaunawar kawo zaman lafiyar Syriyan a inda suka dorawa dakarun gwamnati laifin kai hare-hare bayan an tsagaita wuta daga dukkanin bangarorin biyu.