′Yan adawa sun yi nasara a zaben Kuwait | Labarai | DW | 27.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan adawa sun yi nasara a zaben Kuwait

Rahotanni daga kasar Kuwait na nuni da cewar 'yan takarar jam'iyyar adawa sun lashe wajen kujerun majalisa 20 daga cikin 50 aka yi takararsu.

Manazarta sun danganta sakamakon zaben da fushin jama'a bisa matakan tsuke bakin aljihu na gwamnati.

Da wannan sakamakon zaben na jiya Asabar dai, zai kasance abu mawuyaci ga gwamnati, ta ci gaba da yin sauye-sayen da take yi da nufin rufe gibin kasafin kudin kasar.

Kamfanin dillancin labaru na gwamnati watau KUNA ta ce, 30 daga cikin wadanda suka lashe kujerun majalisar 50, sabbin mutane ne kuma matasa da mace guda, a zaben da kashi 65 daga cikin 100 na wadanda suka cancanci zabe a Kuwaitin suka kada kuri'unsu.