´Yan adawa sun yi barazanar kaddamar da juyin juya hali a Turkeminstan | Labarai | DW | 26.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

´Yan adawa sun yi barazanar kaddamar da juyin juya hali a Turkeminstan

Shugabannnin ´yan adawa na kasar Turkeministan sun ba da sanarwar cewa zasu yi wani juyin juya hali na lumana shigen na kasashen Georgia da Ukraine, idan ba´a aiwatar da sauye sauye na demukiradiya a Turkeministan ba. ´Yan adawa da ke gudun hijira sun yi kira ga KTT da Amirka da Rasha da kuma sauran tsofaffin kasashen TS da su marawa wani shiri na gudanar da zaben shugaban kasa ta hanyar demukiradiya baya. Bayan mutuwar shugaban kasa Saparmurat Niyazov ´yan adawa sun kuduri aniyar tsayar da dan takarar shugaban kasa daya. A yau majalisar al´uma ta kasar zata shawarta don zaben wanda zai gaji shugaba Niyazov wanda ya rasu ranar alhamis bayan ya shafe shekaru 21 a kan wannan mukami.