′Yan adawa sun yi babbar zanga-zanga a Togo | Labarai | DW | 06.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan adawa sun yi babbar zanga-zanga a Togo

Dubban jama'a ne suka fito kan tituna yayin wata zanga-zanga a birnin Lome na kasar Togo da kuma sauran wasu biranen kasar guda 10 inda suke nema da a samu sauyi na mulki a kasar.

Togo Protest #Faure Must Go (Getty Images/AFP/P. U. Ekpei)

'Yan adawa sun yi zanga-zanga a Togo

Kungiyar  Amnesty International ta kiyasta adadin mutanen da suka fito da cewa zai kai dubu 100 a birnin na Lome kamar yadda Aimé Adi da ke a matsayin Darectan kungiyar reshen na Togo ya sanar. Daga nashi bangare madugun 'yan adawan kasar ta Togo Jean-Pierre Fabre cewa ya yi bai taba ganin irin wannan taro a birnin na Lome ba, inda dubban jama'a dauke da kwalaye ke ta furta kalaman nuna kyama ga shugaban kasar Faure Gnassingbé wanda ke mulkin kasar tun daga shekara ta 2005.

Manyan jam'iyyun adawa na Togo akalla guda biyar ne suka kira wannan zanga-zangar, wanda a cewar madugun 'yan adawan ta samu karbuwa sabili da hadin kai na 'yan adawan. Gwamnatin ta Togo dai ta soma bada kai bori ya hau, inda yayin wani taron majalisar ministocin kasar, ta sanar da wasu jerin sauye-sauye da za a aiwatar a kundin tsarin mulkin kasar ciki kuwa har da batun kayyade wa'adin mulki.