´Yan adawa sun lashe zaben ´an majalisar dokokin Czeck | Labarai | DW | 03.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

´Yan adawa sun lashe zaben ´an majalisar dokokin Czeck

Jam´iyar adawa ta masu ra´ayin mazan jiya a Jamhuriyar Czeck, ta lashe zaben ´yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar jiya da kuma yau asabar. Bayan an kammala kidayar kusan dukkan kuri´un da aka kada, jam´iyar ta ´yan mazan jiya karkashin jagorancin Mirek Topolanek, ta samu kashi 35 cikin 100, yayin da jam´iyar FM Jiri Paroubek, wadda ta kwashe shekaru 8 tana jan ragamar mulki a kasar ta samu kashi 32 cikin 100 na yawan kuri´un da aka kada. A halin da ake ciki Topolanek wanda ya kasance mai sukar lamirin KTT ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben. To amma dole sai ya kula kawance da wata jam´iya kafin ya iya kafa gwamnati. Dukkan kananan jam´iyun kasar sun tsallake yawan kuri´u na kashi 5 cikin 100 da suke bukata don samun wakilci a cikin majalisar dokokin jamhuriyar ta Czeck.