′Yan adawa sun ƙauracewa zaɓen Burundi | Labarai | DW | 28.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan adawa sun ƙauracewa zaɓen Burundi

Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza ya zama ɗan takara ɗaya tilo a zaɓen shugaban ƙasa

default

Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza

'Yan takara shida na jam'iyun adawa sun ƙauracewa zaɓen shugaban ƙasa da aka fara yau litinin a Burundi. Wannan janyewar da 'yan adawa sukayi ya sa shugaba mai ci Pierre Nkurunziza ya zama ɗan takara ɗaya tilo.

Janyewar 'yan takarar ya biyo bayan zargin tafka maguɗi ne a zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a watan mayun bana.

Kanfanin dillancin labaran jamus ta ruwaito ƙungiyar cigaban ƙasashen tsakiyar afirka data ƙunshi ƙasashen Tanzaniya da Uganda da Kenya da kuma Rwandan sukayi gargaɗin samun tashin hankali a wannan zaɓe.

Shekaru 45 da samun 'yancin kai, ƙasar ta samu kanta cikin yaƙin basasa, bayan shugabannin ta uku da aka kashe.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Mohammad Nasir Awal