'Yan adawa na zanga-zanga a Banizuwela
April 26, 2017Talla
Wannan zanga-zanga dai ka iya zama mai cike da hadari kasancewa 'yan adawar na son yin tattaki ne har zuwa tsakiyar birnin Caracas wanda kezaman cibiyar jam'iyya mai mulki. A baya dai gwamnatin Shugaba Nicolás Maduro ta yi amfani da karfin tuwo wajen murkushe duk wata zanga-zangar da aka shirya zuwa tsakiyar birnin na Caracas. Hukumomin shari'ar kasar ta Banizuwela dai sun tabbatar da mutuwar mutane 29 a yayin da wasu 437 kuma suka jikkata kana aka kame wasu mutanen 1.289 a yayin jerin zanga-zangar da 'yan adawar suka yi ta gudanarwa, tun daga farkon watan Afrilun da muke ciki da nufin nuna adawarsu da matakin kotun kolin kasar na karbe wani 'yanci na majalisar dokoki, wacce 'yan adawa ke da rinjaye a cikinta.