1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'yan adawa a Kenya sun lashi takobin ƙaddamar da zanga zanga

January 3, 2008
https://p.dw.com/p/Cjdw

Shugaban adawa da ƙasar Kenya Raila Odinga ya lashi takobin ƙaddamar da zanga zanga da ya kira ta mutum miliyan ɗaya a yau Alhamis wadda jama’a da dama ke ganin zata ƙara hura wutar tarzoma da ta ɓarke a ƙasar.

Tashe tashen hankula na ci gaba a Kenya duk da kiraye kiraye daga ƙasashen duniya na sasanta tsakani a rikicin siyasar ƙasar bayan sake zaɓen shugaba Kibaki.

Dukkaninsu ɓangarorin biyu,wato gwamnatin Kibaki da kuma jam’iyar adawa ta Raila Odinga sun zargi juna da kisan kiyashi na kabilunsu. Rahotanni sun ce mutane fiye da 300 suka rasa rayukansu dubbai kuma suka bar gidajensu cikin rikici da ya ɓarke bayan zaɓen. Masu sa ido a zaɓen na ƙasa da ƙasa sun ce wannan zaɓe dai ya gagara cimma ka’idar zaɓe ta ƙasa da ƙasa.