Yan adawa a Japan sunki amincea da shawarar Merkel | Labarai | DW | 30.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan adawa a Japan sunki amincea da shawarar Merkel

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gagara shawo kann shugabanin adawa na kasar Japan game da tura dakarun sojin kasar zuwa Afghanistan.Shugaban jamiyar adawa ta Japan Ichro Ozawa ya ja da cewa ana bukatar izni daga MDD kafin Japan ta shiga harkokin soja a kasar afghanistan.Tun farko a yau din Merkel ta gana da sarkin sarakuna na Japan Akihito a fadarsa dake birnin Tokyo,inda suka tattauan kann batutuwan sauyin yanayi da kuma samarda wasu hanyoyi na samun makamashi.A ranar laraba Merkel ta gana da firaminista Shinzo Abe inda ta sha alwashin cewa kasashen biyu zasu kasance akan gaba a kokarin fitar hayaki masu guba na masanaantu da ake ganin yana haddasa dumamar yanayi a duniya.