1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan adawa a jamus na bukatar ayi bincike

March 5, 2006
https://p.dw.com/p/Bu7e

Jamus

Bisa dukkan alamu a yanzu haka batu daya fi daukar hankalin majalisar dokoki a nan jamus sihine irin rawa da hukumar leken asirin kasar ta taka cikin yakin da aka kaddamar a Iraki a shekasrata 2003.Tuni dai jammiyun adawa guda biyu suka bukaci hukumar da aka nada domin binciken wannan lamari a majalisar,daya gaggauta gudanar da bincike.Sakataren jammiyar adawa ta FDP Jurgen Koppelin,yace jammiyarsa itama zata bada nata gabatarwa a hukumance a gobe jumma.Zaayi gudanar da wannan bincike ne idan jammiyun adawa guda uku na kasar sun gabatar da bukatar yin hakan.