1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

’Yan ƙungiyar Tamil Tigers na Sri Lanka, sun janye daga yarjejeniyar tsagaita wuta ta shekara ta 2002.

July 31, 2006
https://p.dw.com/p/BuoR

’Yan tawayen ƙungiyar nan ta Tamil Tigers ta ƙasar Sri Lanka, sun ba da sanarwar janyewa gaba ɗaya daga yarjejeniyar tsagaita wutar da suka cim ma da gwamnatin ƙasar a cikin shekara ta 2002. Shugabannin ƙungiyar sun ce hare-haren da dakarun gwamnatin ke ta kai musu daga sama da kuma ƙasa tun makon da ya gabata, na nuna cewa, yanzu an koma yaƙin basasa. A yau ma rahotanni sun ce an yi wani mummunan ɗauki ba daɗi tsakanin ɓangarorin biyu, inda dakarun gwamnatin suka yi asarar sojoji 5, sa’annan wasu 6 kuma suka ji rauni. Babu dai wani tabbataccen labari kan asarar da ’yan tawayen suka yi. Gwamnatin Sri Lankan dai ta ce, har ila yau tana kiyaye yarjejeniyar tsagaita wutar. Rikicin da ake yi yanzu ya ɓarke ne yayin da dakarun gwamnatin ke yunƙurin hana ’yan tawayen kame wasu muhimman tashoshin samad da ruwan sha na ƙasar.

A halin da ake ciki dai, ƙasashen Finland da Dennmark, sun ce daga ran 1 ga watan Satumba ne za su janye jami’ansu da suka tura Sri Lankan, don sa ido kan kiyaye yarjejeniyar tsagaita buɗe wutar.