Yamutsi a zaben ´yan majalisar dokokin Masar | Labarai | DW | 26.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yamutsi a zaben ´yan majalisar dokokin Masar

A cikin wani yanayi na yamutsi an fara kada kuri´a a zagaye na gaba na zaben ´yan majalisar dokokin Masar. Wasu kotuna sun ba da umarnin rufe wasu rumfunan zabe a yankin kusa da Kogin Nilu daya daga cikin wuraren da jam´iyar ´yan adawa ta ´yan´uwa musulmi ke da rinjaye. Rahotannin sun ce ´yan sanda sun tursasawa masu zabe inda suka yi amfani da karfin hatsi wajen hana wasu kada kuri´a a yankin. Bugu da kari an tsare wasu magoya bayan jamiyar ´yan´uwa musulmi, wadda ta samu yawan kuri´u fiye da jam´iyar shugabankasa Hosni Mobarak a zagayen zaben ´yan majalisar dokokin da aka gudanar ranar lahadi da ta gabata. Yanzu haka dai jam´iyar na da kujeru 44 yayin da jam´iyar gwamnati dake ci ke da kujeru 120. A ranar 7 ga watan desamba za´a gudanar da zagayen karshen na zaben.