Yammacin Afrika tayi a dabo da cutar Ebola
January 14, 2016Talla
Kwararru da ke cikin hukumar ta WHO, sun kuma yi gargadi cewar duk da nasarar da aka samu, to kuwa a hannu daya dole ne a cigaba da taka tsan –tsan don kaucewa sake bullar cutar ta Ebola.
Bayanin kakkabe kwayar cutar ta Ebola a yammacin Afrika ya shafe kwanaki 42 bayan tabbatar da bullar kwayar cutar ta karshe a kasar Laberiya, dake kasancewa kasa ta karshe a yammacin Afrika da cutar ta fi kamari.
Fiye da mutane sama da dubu goma sha daya ne suka mutu sakamakon bullar kwayar cutar ta Ebola a shekara ta 2013, a yayin da karin wasu sama da dubu 28 suka kamu da kwayar cutar.