Yakin ′Yancin Kan Aljeriya | Siyasa | DW | 01.11.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yakin 'Yancin Kan Aljeriya

A daidai ranar daya ga watan nuwamban shekarar 1954 ne al'umar Aljeriya suka gabatar da matakin farko a fafutukar kwatar 'yancin kan kasarsu daga hannun mulkin mallakar Faransa

A daidai jajibirin wani biki na ‚yan darikar katolika al’umar Aljeriya suka ta da kayar baya, inda suka bi dufun dare suna cunna wa gidajen Faransawa ‚yan kaka-gida wuta. A lokaci guda kuma nakiyoyi suka rika yin bindiga a fadar mulki ta Algiers da sauran garuruwa da biranen kasar Aljeriyar dake karkashin mulkin mallakar Faransa. A lokacin da yake bayani game da haka Farfesa Hartmut Elsenhans, masani akan al’amuran siyasa cewa yayi:

Yakin ya fara ne tare da daukar matakin kai hare-hare a dukkan sassa na kasar Aljeriya bisa manufar bayyanarwa a fili cewar wannan yaki ne da ya shafi illahirin al’umar kasar, amma ba wasu daidaikun yankuna ko kabilunta ba.

Kungiyar famar neman ‚yancin kan Aljeriya ta FLN ita ce ke da alhakin gabatar da wannan mataki a ranar daya ga watan nuwamban shekara ta 1954 bisa manufar ‚yantar da kasar daga mulkin mallakar Faransa na tsawon shekaru 120. Ita dai faransa tun bayan da ta kutsa kai zuwa Aljeriya a shekara ta 1830 ta raba harabar kasar zuwa larduna uku bisa ikirarin cewar Aljeriya wani bangare ne na kasar Faransa. Amma fa su kansu ainifin ‚yan kasar Aljeriyar ba a girmama hakkinsu, inda aka mayar da su tamkar ‚yan kasa masu daraja ta biyu a daura da Faransawa ‚yan kaka-gida. Har ya zuwa shekara ta 1947 al’umar musulmin Aljeriya su miliyan tara ba su da hakkin shiga zabe, ba su da ikon halartar jami’o’i ballantana a yi ba tu a game da rike wani babban mukami a kasar. Ala-tilas akasarinsu suka shiga ci rani a manyan gonaki na manoma Faransawa.

Larabci ne harshe na, musulunci ne addini ne kuma Aljeriya kasa ta ce.

Wannan lafazin ya fito ne daga bakin Sheikh Abdelhamid Ben badis, wanda kuma ya zama jigon masu fafutukar neman ‚yancin kan kasar Aljeriya. Kuma duk da banbance-banbancen manufofin dake akwai tsakanin masu fafutukar kwatar ‚yancin kan Aljeriyar, amma an samu kakkarfan hadin kai tsakaninsu domin tinkarar dakarun Faransa. An dai yi kimanin shekaru bakwai ana gwabza wannan yaki tare da mummunan zub da jini da halaka kimanin kashi 10% na al’umar Aljeriya kafin Faransar ta ba ta mulkin kanta a ranar biyar ga watan yulin shekarar 1962.