Yakin Neman Zaben Majalisar Turai | Siyasa | DW | 19.05.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yakin Neman Zaben Majalisar Turai

A ranar 13 ga watan yuni mai kamawa ne za a gudanar da zaben majalisar Turai. To sai dai kuma mutane ba su dauki majalisar da muhimmanci ba, lamarin dake ci wa wakilanta tuwo a kwarya

Wakilan jam'iyyar Greens a majalisar Turai

Wakilan jam'iyyar Greens a majalisar Turai

A daidai wannan lokaci da aski ke dada karatowa gaban goshi dangane da zaben na majalisar Turai, ‚yan takarar ke jin radadin lamarin. Suna kewayawa sassa dabam-dabam domin yakin neman zabe, amma fa a daya bangaren sun farga cewar babu wani tasiri da mutane suka gani a game da ayyukansu a shekaru biyar din da suka gabata. An ji irin wannan bayanin daga bakin Karin Jöns #yar takarar jam’iyyar SPD a Bremen. Ta ce babban abin takaici shi ne kasancewar ta kasa cusa ra’ayin kaunar manufofin Turai a zukatan jama’a a cikin shekaru goma na aikinta a majalisar Turai, duk kuwa da cewar, bisa sabanin da yawa daga cikin takwarorinta na majalisar, ta kan shirya ganawa akai-akai da talakawan kasa a maimakon rarraba kasidu tsakanin jama’a. Babu wani mai kula da ita, idan an kwatanta da yadda mutane ke ba da la’akari da wakilan majalisar dokoki ta Bundestag, sai fa idan lokacin zabe ya karato. To sai dai kuma, kamar yadda aka ji daga bakin Thomas Mann, wakilin majalisar Turan daga jihar Hesse, wannan ba abin mamaki ba ne saboda duka-duka wakilai 99 ne Jamus ke da ikon turawa zuwa majalisar alhali kuwa kasar na da yawan al’uma na miliyan 80. Ya ce shi kansa yana wakiltar mutane ne kimanin miliyan biyu da dubu metan, wanda a sakamakon haka da wuya ya iya tuntubar kowa da kowa. Wani abin da ka iya fito da wakilan majalisar ta Turai a bainar jama’a shi ne wata dama ta shiga mahawara a gidajen telebijin. Domin ta haka ne zasu iya wayar da kan mutane a game da muhimmancin ayyukan majalisar tasu ga dukkan yankunan Turai da lamarin ya shafa. Kimanin kashi 80% na abubuwan da majalisar tarayya ta gwamnonin jiha a nan kasar ke zartaswa suna da nasaba da abubuwan da aka zartas a matsayi na Kungiyar Tarayyar Turai baki daya. Misali duk wani hukuncin da KTT zata yanke a game da ka’idojin aiwatar da magunguna na chemicals, abu ne da zai shafi jihohin kasar nan da dama. Wakilan majalisar Turai suna taka muhimmiyar rawa wajen kare bukatun yankunan da suke wakilta a irin wannan zartaswa. A halin yanzu haka wakilan Jamus a majalisar suna bakin kokarinsu wajen ganin lalle sai an ware kasar domin zama babbar cibiyar al’adun nahiyar Turai a shekara ta 2010. Daga cikin biranen kasar dake gwagwarmayar neman wannan matsayi kuwa har da Bremen da Augsburg da kuma Kassel. Kimanin kashi 70 zuwa 80% na kudurorin Kungiyar Tarayyar Turai majalisar ke da hannu wajen zartar da su. Kuma majalisar zata samu karin tasiri da zarar an gabatar da daftarin nan na tsarin manufofi bai daya tsakanin kasashen Kungiyar Tarayyar Turai. Amma fa dukkan wadannan abubuwa ne da ya kamata a wayar da kan jama’a game da su saboda su ankara da muhimmancin majalisar kamar yadda dukkan wakilanta suka hakikance.