Yakin neman zabe a Senegal | Siyasa | DW | 04.02.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yakin neman zabe a Senegal

yan takara 15 a Senegal sun shiga Kampain na zaben shugaban kasa ranar 25 ga watan februaru.

a ƙasar Senegal , yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, da za a gudanar ranar 25 ga watan da mu ke ciki ya kankama

A tsawan kwanaki 21, yan takara daban-daban da su ka haɗa da shugaba mai ci yanzu Abdullahi Wade, za su tallata kansu, ga al´uma.

Baki ɗaya yan takara 15, su ka shiga gwagwarmayar neman jagorancin Senegal.

Bayan shugaba Wade, ɗan shekaru 80 a dunia,da ke buƙatar yin tazarce, akwai tsofan Praminista Mustafa Niass mai shekaru 67 daga jam´iyar AFP, da Idrissa Seck shima tsofan praminista, da Usman Tanor Dieng na jam´iyar gurguzu.

Masu kulla da harakokin siyasa a Senegal, na ɗaukar wannan yan takara 3, a matsayin wanda za su hadasa babban ƙalubale ga shugaba Abdulahhi wade.

Da dama daga manazarta na kyauttata zaton Wade za shi tazarce duk kuwa da zargin da ya sha na rasin taka rawar a zo a gani a tsawan mulkin sa.

A jimilce masu zaɓe kimanin milion 4 a ke sa ran za su kaɗa ƙuri´aranar 25 ga watan Februaru, domin raba gardama tsakanin yan takara 15.

A halin yanzu dai, su na ci gaba da shirya taruruka a jihohin ƙasar baki ɗaya, kuma ya zuwa yanzu komai na tafia salin alin.

Ƙasar Senegal, na matsayin madubi a nahiyar Afrika, ta fannin tsarin mulkin demokradiya.

Sabaninda dama daga kasashenAfrika, Senegal ba ta taɓa samun juyin mulki ba,da ƙarfin soja, tun samun yancin kanta daga turawan mulkin mallaka na France, a shekara ta 1960.

Sanan ta daya daga kurin kasashenAfrika inda shugaba mai rike da ragamar mulki ya fadi a zabe, inda dai ba manta ba,a zaɓen shugaban ƙasa na shekara ta 2000, madugu yan adawa, Abdullahi Wade, ya kada shugaban ƙasa na wacen lokaci, wato Abdu Diouf, a cikin zaɓe mai tsabta.

 • Kwanan wata 04.02.2007
 • Mawallafi Yahouza S.Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtwP
 • Kwanan wata 04.02.2007
 • Mawallafi Yahouza S.Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtwP