Yakin neman zabe a Jamhuriya Benin | Labarai | DW | 17.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yakin neman zabe a Jamhuriya Benin

Yau ne a kasar Benin a ka fara yakin neman zabe, a zaben shugabankasar da za a yi ranar 5 ga wata mai kamawa idan Allah ya kai mu.

Saidai, akwai rudani da dama, a dangane da shirye shiryen wannan zabe, a kan haka,shugaba hukumar zabe mai zaman kanta , Sylvain Nouwatin,ya kiri yan siyasa da su kwantar da hankula, su kuma gudanar da yakin neman zabe cikin tsabta da sanin ta kamata.

Baki daya, mutane kussan million 4 ne, za su kada kuri´a, a wannan zabe.

Tun bayan komawar Jamhuriya Benin, bisa tafarkin demokradiya a shekara ta 1990,wannan, shine karro na 4, da al´umma za ta zaben shugaban kasa.

A jimilce ,yan takara 26 ne, su ka shiga neman maye gurbin shugaba mai ci yanzu Mathieu Kereku, dan shekaru 72 a dunia, wanda kuma a wannann karo, bai ajje takara ba,hakazalika, babban abokin adawar sa, Nicephore Soglo.