Yakin Neman zabe A Guinea-Bissau | Siyasa | DW | 31.05.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yakin Neman zabe A Guinea-Bissau

A karkashin wani gurbataccen yanayin siyasa aka gabatar da yakin neman zaben shugaban kasa a Guinea Bissa ta yammacin Afurka

Tsofon shugaban Guinea Bissau Kuma Yala

Tsofon shugaban Guinea Bissau Kuma Yala

A ranar asabar da ta wuce ne aka gabatar da matakin farko na yakin neman zaben shugaban kasar Guinea-Bissa da aka shirya gudanarwa a ranar 19 ga watan yuni. ‚Yan takara 17 ne ke da shirin kalubalantar juna, 12 daga cikinsu a karkashin tutar jam’iyyun siyasa sannan ragowar biyar kuma a matsayin ‚yan takara masu zaman kansu, a tsakaninsu akwai tsaffin shuagabanni uku da kuma wasu tsaffin piraministoci guda biyu. To sai dai kuma yakin neman zaben an gabatar da shi ne a daidai lokacin da kasar ke cikin wani gurbataccen yanayin siyasa. A makon jiya jami’an tsaron kasar sun murkushe wani yunkuri na juyin mulkin da tsofon shugaba Kumba Yala ya shirya. Tsofon shugaban, wanda a kusan shekaru biyun da suka wuce ne aka kifar da gwamnatinsa ya samu rufa baya daga wasu sojojin domin kutsawa fadar mulki da mamayar ginin. Amma a cikin sa’o’i kalilan sojojin suka cimma nasarar shawo kansa domin ficewa daga fadar mulkin. Bayan wannan yunkuri da a yanzu maganar tsofon shugaba Kuma Yala ne ke shiga kanun labarai. Shi da tsaffin shuagabanni biyu da suka hada da Nino Vieira da Malam Bacai Sanha, da kuma tsaffin piraministoci biyu, daya daga cikinsu ake kyautata zaton cewar zai lashe zaben. Ba tare da rufa-rufa ba shugaban Abdoulaye Wade na kasar senegal ke goya wa Kuma Yala baya. Wannan mataki nasa na fuskantar suka da kakkausan harshe daga kungiyoyi masu zaman kansu. A cikin hira da tashar DW Jamel Hndem, shugaban wata gamayya ta kungiyoyi na cikin gida masu zaman kansu ya ce dukkan kasashen Senegal da Guinea dake goya wa Kumba Yala baya, suna da wata maslaha ce ta tattalin arziki da suke bukatar cimmawa a kasar Guinea-Bissau. An saurara daga wasu jami’an siyasa dake da nasaba da jam’iyyar gwamnati mai mulki suna bayyana cewar dalilin neman kusantar juna da wadannan kasashe makobta ke yi da Guinea-Bissau shi ne binciken rijiyoyin mai da wani babban kamfani na ketare ke yi a kasar yanzu haka. Ko da yake da yawa daga jami’an siyasar na amfani da kabilanci domin neman goyan baya a yakinsu na neman zabe, amma akasarin ‚yan takarar sun fi mayar da hankalinsu ne ga batutuwa da hadin kai da kwanciyar hankali da kuma neman ci gaban kasarsu. An ji irin wannan bayanin daga tsofon shugaba Kumba Yala, inda yake cewar:

‚yanci da walwala da adalci da tsage gaskiya da hakuri da juna, shi ne muhimmin abin dake gabanmu. Muna bukatar wani yanayi na zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Akwai da yawa daga cikin jami’an siyasar dake fargabar fuskantar tashe-tashen hankula lokacin yakin neman zaben. An ji wannan bayanin daga Antonieta Rosa Gomes, wacce ta sha shiga takarar zaben amma ba tare da nasara ba. Shi ma Mario Cabral, kwararren masanin al’amuran siyasa ya bayyana irin wannan fargaba tare da bayanin cewar mai yiwuwa ma a saka ayar tambaya a game da sakamakon zaben. Ya kara da cewar:

Sanin kowa ne cewar a kowane zaben da aka gudanar a kasashen Afurka sai an saka ayar tambaya a game da sakamakonsa. Kuma ina kyautata zaton cewar hakan zai faru a Guinea-Bissau.

Tuni KTT ta tura tawagar farko ta jami’an sa ido akan zaben na Guinea-Bissau.