Yakin neman zabe a Faransa | Labarai | DW | 04.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yakin neman zabe a Faransa

Yar takarar kujerar shugaban kasar faransa daga jammiyyar masu sassaucin raayi Segolene Royal,tayi gatrdin cewa Faransa zata iya fada wasu sabbin rigingimu a unguwannin baki ,idan har Nicholas Sarkozy na jammiyyar masu raayin rikau ya lashe zagaye na biyun zaben shugaban kasar da zai gudana a ranar lahadi.Royal ta fadawa gidan radion RTL cewa ,Sarkozy zai kawo rudadi cikin faransa.An dai soki kalaman ministan harkokin cikin gidan Faransan,na kiran matasa yan tarzoma gabannin tashe tashen hankula da suka barke a unguwannin baki a 2005.A yanzu haka dai Sarkozy na da rinjayen magoya baya da kashi 8 daga cikin 100,akan Royal.