Yakin kwato birnin Raqqa na Siriya ya kankama | Labarai | DW | 07.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yakin kwato birnin Raqqa na Siriya ya kankama

'Yan tawayen Siriya da ke samun goyon bayan Amirka sun shirya tsaf don kwato birnin Raqqa.

Syrien SDF PK Sturm auf Rakka (Getty Images/AFP/D. Souleiman)

Jihan Sheikh Ahmed (a tsakiya), mai magana da yawun kungiyar Syrian Democratic Forces

A daidai lokacin da ake ci gaba da gumurzu da nufi fatattakar mayakan kungiyar IS daga birnin Mosul na Iraki, yanzu haka wani kawancen mayakan Kurdawa da na Larabawa na kara dannawa birnin Raqqa da ke zama wata tungar 'yan IS a kasar Siriya. Sojojin na Kurdawa da Larabawa suna kan hanyarsu zuwa Raqqa don kara matsa lamba kan masu ikirarin jihadin na IS. Kawancen kungiyar da ake kira Syrian Democratic Forces da ke samun tallafin Amirka na da mayaka kimanin dubu uku.

Jihan Sheikh Ahmed ita ce mai magana da yawon kungiyar wadda ta bada sanarwar fara gagarumin yaki da nufinsa shi ne ceto birnin Raqqa da kewayensa daga hannun 'yan ta'addar IS.

Sai dai matakin na fuskantar kace-nace na muradun wasu kasashe, a yayin da Amirka ke mara baya ga Kurdawa, ita kuwa kasar Turkiyya na yi musu kallon 'yan ta'adda.