1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yakin Kasar Kongo

Al'amura na dada yin tsamari a kasar Kongo amma har yau babu wani martani na a zo a gani da kafofin kasa da kasa suka mayar domin dakatar da wannan mummunan ci gaba

Yaki a kasar Kongo

Yaki a kasar Kongo

Da kamata yayi tun da farkon fari a fahimci alkiblar da aka fuskanta a daidai lokacin da shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame ya kada baki yana mai fada wa jami'an diplomasiyyar MDD cewar duk mai bukatar zaman lafiyar yankin kuryar tsakiyar Afurka to kuwa wajibi ne ya fara da gabatar da matakin yaki. Wannan katobarar ta Kagame ta faru ne a misalin wata daya da ya wuce, amma ba wanda ya ba da la’akari da ita. Da kamata yayi tun daga sannan a fahimci manufar shugaban na mitsitsiyar kasa ta Ruwanda a game da aniyarsa ta tura sojojinsa zuwa Kongo karo na uku tun abin da ya kama daga shekarar 1996. Kutsen da sojojin Ruwandan suka yi a 1998 ya taimaka wasu kasashe shida suka shiga aka dama da su a cikin abin da aka kira wai "Yakin Duniya na Farko A Nahiyar Afurka," wanda yayi sanadiyyar salwantar rayukan mutane kusan miliyan hudu. Ba a kuwa taba samun salwantar rayuka irin shigen wannan ba tun bayan yakin duniya na biyu. Kuma ko da yake a hukumance an kawo karshen yakin, amma a kullu-yaumin ana fuskantar barazana da kisan ba gaira akan mata da yara kanana. Yakin ya dauki wani sabon fasali, saboda a yanzun ba yaki ne tsakanin Tutsi da Hutu ko Hema ba, yaki ne mai sarkakiyar gaske, wanda kuma yake nema ya zama gagara-badau. Manufar Kagame a wannan karon shi ne fadada angizonsa zuwa gabacin Kongo, bisa sabanin yadda lamarin ya kasance a zamanin baya inda yake ikirarin fatattakar dakarun Hutu dake da alhakin kisan ‚yan Tutsi sama da dubu 800 a kasar Ruwanda. Muhimmin abin da yake kwadayi shi ne dora hannu akan albarkatun kasa da Allah Ya fuwace wa Kongo. Shugaban na Ruwanda dai ya cimma biyan bukatarsa ta farko a game da ta da zaune tsaye da haddasa yamutsi a kasar Kongo, wacce a sakamakon haka take fama da rarrabuwa da dada kutsawa cikin hali na kaka-nika-yi game da makomarta. Dangane da sojan kiyaye zaman lafiya kimanin dubu 10 da MDD ta tsugunar a Kongon kuwa, tuni suka zama tamkar masu yawon bude ido ne kawai. Wani mummunan ci gaba ma shi ne zargin da ake wa sojojin na ci da gumin ‚yan gudun hijirar dake fama da mawuyacin hali na rashin sanin tabbas. Shi kuma kwamitin sulhu na MDDr sai lalube yake yi a cikin dufu da barazanar kakaba wa Ruwanda takukumi, amma ba tare da tabuka kome ba. Kagame dai ya kai kasar Kongo ya baro su kuma kafofi na kasa da kasa sun zura na mujiya suna kallonsa yana cin karensa babu babbaka. Kuma abin takaici shi ne kasancewar ba a koyi darasi daga ta’asar kisan kiyashin da ya faru a kasar Ruwanda shekaru goman da suka wuce ba.