1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki mafi tsawo

Abba BashirAugust 7, 2006

Yaki mafi tsawo a Tarihin Duniya

https://p.dw.com/p/BvVK
Soja a filin daga
Soja a filin dagaHoto: AP

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malam Abubakar Salmanu, Birnin Jidda, a kasar Makkatul-mukarramah. Malamin ya ce ; Shin, wane Yaki ne mafi tsawo a tarihin wannan Duniya tamu?

Amsa : To Malam Salmanu, yakin dai da aka yi shekaru Daruruwa ana yi, shine yakin da aka dauki tsawon lokaci ana yi ana tsagaitawa tsakanin kasar Ingila da kasar Faransa, tun daga shekarar 1337 zuwa 1453, wato a takaice an shafe kusan shekaru 116 ana fafatawa.

An fara wannan yaki ne a lokacin da sarkin ingila wanda ake kira da suna Sarki Edward na uku, ya kalubalanci gadon sarautar Faransa, kuma ya mamaye yankin arewa maso yamma na kasar ta Faransa. Sarkin da ya gaji Sarki Edward shi ne Sarki Richard na biyu, shi ma ya ci gaba da wannan yaki, haka zalika Sarki Henry na hudu wanda ya tumbuke Richard daga Sarauta, shima ya ci gaba da gwabza yaki da faransawa.Sarki Henry na biyar shine wanda ya zama Sarkin Ingila bayan Sarki Henry na hudu,shine kuma wanda ya ci Faransawa da yaki a yakin da ake kira da suna “Agincourt’’ in da ya nada mukaddashinsa a kasar ta Faransa.

Bayan shekaru da dama, Sarkin Faransa wato Charles na biyar, ya dawo da yaki sabo, inda ya koma yakar Ingila tare da taimakon Kasar Scotland, kuma kasar ta Faransa daga baya ta samu nasarar yake-yake da dama musamman ma a shekarar 1429, amma dai ba’a samu wata cikakkiyar nasara ba sai a shekarar 1436, lokacin da Faransawa suka yanto Birnin Faris daga karkashin Mulkin Ingila, Sannan kuma a shekarar 1453 Faransa ta kori Ingila kwata-kwata daga yankinta.

Yaki na biyu da yake rufawa yakin Ingila da Faransa baya, shi ne yakin Lardin Aceh, ko da yake dai akwai yar tababa daga bangaren masana tarihi game da tsayin da ake cewa yakin na lardin Aceh ya yi, wato tsakanin Al’ummar Aceh na Kasar Andulisiya (Indonesia) da kuma Al’ummar Kasar Holland. Da farko dai Holland ce ta kaddamar da yaki akan Al’ummar Lardin Aceh, a shekara 1873, to daga nan ne fa yaki ya ci gaba yana yi yana lafawa na tsawon shekaru da dama. Wasu masana tarihi sunce yaki ya kare ne a shekarar 1903, amma dai a Hukumance Al’ummar Kasar Holland basu kwashe ya nasu-ya nasu ba har sai a shekarar 1942. Sabodahaka za’a iya cewa yakin Lardin Aceh ya dauki tsawon shekaru 30 ko kuma 69.

To idan muka komo yake-yaken da suka faru a karni na ashirin, babu wani Mutum da zai iya cewa ga yakin da ya fi tsawo, domin kuwa wadansu har yanzu ana nan ana ci gaba da su.Misali yakin da ake yi tsakani Yahudawa da Falasdinawa, yaki ne da ya samo asali tun a shekara 1946, wato bayan yakin duniya na biyu, lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta tsaga yankin Falasdinu, inda aka baiwa Yahudawa kashi hamsin da biyar bisa dari na Falasdinu, su kuma Falasdinawa aka basu kashi Arba’in da biyar bisa dari, sabodahaka sai suka ce basu yarda ba.To daga nan ne fa yaki ya fara har ya zuwa yau, kusan kimanin shekaru sittin kenan ana cikin wannan hali.

Akwai kuma rikicin kasar Sudan na yakin-basasa wanda aka fara tun a shekarar 1955, inda yanzu haka an dauki kusan shekaru Hamsin da daya (51) ana wannan gumurzu.Hakazalika ita ma Kasar Goatemala ta fada gararin yakin-basasa wanda ya dauki kusan shekaru 36 tun daga shekarar 1960 zuwa 1996.Kai babu ko shakka , abin bakin ciki ne idan aka dubi yadda tarihin Duniya ya cika da yake-yake masu tsawo,domin kuwa baya ga wadanda mu bayyana a baya, har’ila yau akwai yakoki irin su Yakin nan na Kasar Greece mai tarihi wanda ya dauki shekaru (27) da kuma Yakin Vietnam wanda akai shekaru Goma-sha-takwas ana yi.Banda kuma rikicin da yaki ci yaki cinyewa fiye da shekaru talatin da uku (33) a yankin“Northern Ireland’’. Ni dai a gani na wadannan yake-yake dukkanin su, yake-yake ne masu tsawo kwarai da gaske.