1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin kare muhalli a Nijar

Abdoulaye mamane Amadou / LMJAugust 3, 2016

Matasan mawaka a Jamhuriyar Nijar sun dukufa wajan wayar da kan jama'a illolin da ke tattare da sauyin yanayi, sakamakon sare itatuwa da ma sauran abubuwa da ke taimakawa wajen gurbata yanayi.

https://p.dw.com/p/1Jb2Z
Mawaki mai fafutukar kare muhalli a Nijar Malam Ousmane Abdourahmane
Mawaki mai fafutukar kare muhalli a Nijar Malam Ousmane AbdourahmaneHoto: DWA. Mamane Amadou

Rukunin mawakan dai na yin kira ga jama'a a kan su hada hannu domin kaucewa fadawa matsalar ta gurbatar yanayi ta hanyar wakoki da tuni suka fara samun shauki da karbuwa ga al'umma. Matasan da daukacinsu ba su wuce shekaru 28 ba, na daga cikin tarin rukunin matasan da ke wakokinsu a baya da tsarin hululu ko Rap sai dai sakamakon kamarin matsalar yanayi da gurbacewarsa ya sa sun sauya akalar waken nasu zuwa wani sabon salon yin waka da nufin isar da sako zuwa ga al'umma. Babban burin matasan shi ne na yin batun muhallin cikin wani sabon salo ta yanda zai ja hankali domin kubutar da kasar fadawa cikin wani yanayi da al'umma su da kansu ke haifarwa. Malam Ousmane Abdourahmane mai lakabin Carle daya ne daga cikin matasan mawakan ya kuma ce:

Gurbata muhalli cikin rashin sani

"Wadansu a cikin rashin sani da kansu suke haifar da sauyin yanayi su kuma sanya ya yi kamari sosai, a wasu lokutan a kan samu ruwan sama ya sauko fiye da yanda aka saba, haka na su na janyo kwararowar hamada ta hanyar kashe itace ba tare da sun lura ba, ita kuma hamada tana kara kawo sauyin yanayi."

Sai dai wani abin mamaki shi ne matasan an fi sanin su ne da rera wakoki kuma na matasa, sai kuma gashi sun rikide tare da komawa yin wakokin jan hankali da nufin isar da wani sako, Carle ya ce ba abin mamaki ba ne:

"Ni ina ganin sauyin yanayi baya da wani matashi ko mawaki, abu ne da ya shafi kowa ya kuma shafi duniya. Ke nan mu duka ne ya kamata mu tashi tsaye domin mu inganta duniya ta yanda za ta samu daidaito."

Tuni dai wasu kungiyoyin matasa masu gwagwarmaya kan inganta muhalli suka dafawa rukunin mawakan baya da nufin ganin an gudu tare an kuma tsira tare wajen cimma babban burin kyautata muhalli. Malam Mamane Sani Abdoulaye kusa ne a kungiyoyin matasa da ake kira JVE ya kuma ce:

"Wadanda suka fi fuskantar matsalolin na sauyin yanayi da ma kalubale su ne matasa da mata da yara kanana, to kenan idan aka bi ta hanyar wadannan mawakan sakon zai iya saurin isa inda ake son ya kai."

Mawaki Malam Ousmane Abdourahmane da shugaban kungiyar matasa da ke tallafa masa Malam Mamane Sani Abdoulaye
Mawaki Malam Ousmane Abdourahmane da shugaban kungiyar matasa da ke tallafa masa Malam Mamane Sani AbdoulayeHoto: DWA. Mamane Amadou

Ambaliyar ruwa da kwararowar hamada

Wannan wakar dai na zuwa ne a yayin da galibin wadanda masana ke zargi da cutar da muhalli ke da karancin ilimi kana suka jahilci lamarin, duba da yadda suke haifar da mummunar barna kuma galibi yawancinsu na zaune ne a yankunan karkara. Jamhuriyar Nijar dai na daya daga cikin kasashen da ke fuskantar matsalar gurbatar muhalli inda yake haifarwa kasar yawaitar ambaliya da kwararowar hamada da fari ga kuma takaituwar filin noma da kiyo kana ga rashin wadattacen cimaka ga al'ummar kasar da alkalumma ke kiyasta cewa sun haura mutum miliyan 17.