1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da cutar Malaria

Jamilu SaniMay 11, 2004

Hukumar lafiya ta duniya da hadin kan wasu hukumomi na majalisar dikin duniya,sun ce za'a bulo da sabin matakan yaki da cutar Malaria kafin nan da shekara ta 2015.

https://p.dw.com/p/Bvjj
Yaki da cutar Malaria da sauro ke yadawa
Yaki da cutar Malaria da sauro ke yadawaHoto: AP

A halin yanzu dai kwayoyin cutar da sauro ke yadawa a jinin bil adama na neman zama babar barazana ga harkokin kula da lafiya a duniya baki daya kamar dai yadda cutar Aids ko HIV ta zamanto babar musiba ga lafiyar bil adama.

Kwayoyin cutar da sauro ke dauke da su da aka fi sanni da cutar Malaria ko cutar zazaben cizon sauro,da mutanen kasar Italiya ke yiwa lakabi da gurbataciyar Isska,na afkuwa ne a lokacin da bil adama ya shaki isska mai guba mai dauke da kwayoyin cutar Malaria,daga nan ne kuma kwayoyin cutar Malaria ke kama kafofin nunfashin bil adama.

A shekara ta 1880,masana ilimin kimiya sun gudanar da bincike kann kwayar cutar Malaria da ake kira Palasmodium,wace kuma aka tabatar da cewa ke sawa mutum ya kamu da cutar malaria.

Cutar dai ta Malaria ko kuma zazaben cizon sauro,na afkuwa ne a kasahen duniya dake da yanayi mai zafin gaske,da suka kunshi kashi 40 daga cikin dari yawan alumar da ake da su a duniya baki daya. Koda Yake an yi kokarin murkushe cutar malaria a tsakiyar karni na 20,amman kuma masana harkokin kula da lafiya na fargabar cewa mai yiwa ne wanan cuta ta cigaba da yaduwa a tsakanin aluma a sabili da matsalolin da ake fuskanta na karuwar dumamar yanayi a duniya baki daya.

Cutar dai ta Malaria kann halaka alumomin da yawan su zarta miliyan daya a duk shekara,ko kuma mutane 3,000 a duk rana ta Allah.

An dai baiyana cewa kashi chasa’in daga cikin dari na yaduwar cutar Malaria,sun fi afkuwa ne a kasahen Afica dake kudu da hamadar Sahara.

A duk shekara dai akala mutane miliyan 300 ke kamuwa da cutar Malaria a duk shekara.

A mafi yawan lokuta cutar ta Malaria ko kuma zazaben cizon sauro,yafi kama kanan yara da shekarun su na haihuwa ke kasa da biyar,sai kuma mata masu juna biyu harma da yayan da ba’a haifa ba hade da tsafi da shekarun su na haihuwa suka yi nisa.

Alamun kamuwa da cutar dai ta Malaria sun hadar da zazabe mai zafi,ciwon kai kuma lo da kuma wasu sauran alamun dake daukar tsawon kwanaki 14 kafin cutar ta fara kama bil adama.

Ga dukanin mutumin da ya kamu da cutar malaria ana bukatar kwayoyin maganin yaki da wanan mugunyar cuta cikin hanzari.

Kwayoyin cutar Malaria na saurin lalata kwayoyin halitun dake cikin jini tare kuma da haihar da karancin jini da kuma toshe hanyoyin gudanawar jini,inda isskar Oxygen ke bi zuwa kwakwalwar bil adama.

Mace sauro da aka fi sanni da Anopheles ke yada cutar ta Malaria a jikin bil adama a lokacin da ta sha jininsa,za kuma ta iya yadda wanan cuta a jikin mutum mai lafiya a lokacin da machen sauron ta ciji jikinsa.

An dai bukatar fiye da dola biliyan 12,don yaki da cutar Malaria a nahiyar Africa duk shekara.