1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya

Salisou BoukariMarch 25, 2016

Fadar gwamnatin Tarayyar Najeriya ta fitar da wani rahoto da ke nuni da cewar kamfanoni 300 ne da kuma dai-daikun mutane ke da hannu a badakalar kudaden da aka ware domin sayen makamaki.

https://p.dw.com/p/1IJlN
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Getty Images/AFP/E. Piermont

Rahoton ya nunar da cewa daga cikin dai-daikun mutanen har da manyan sojoji da ake zargi da laifin karkatar da akalar makudan kudi da yawansu ya kai Naira miliyan dubu 48, kwatankwacin Euro miliyan 215. Wannan zargi ya fito ne bayan binciken da shugaban kasar ta Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umarnin aiwatar wa kan abin da ya shafi kwangiloli na harkokin tsaro da aka bayar daga shekara ta 2011 zuwa 2015 a kokarin da yake na yakar cin hanci da rashawa, wanda ya hana kasar da ke a matsayin ta daya a fannin arzikin man fetir a nahiyar Afirka cigaba. Wannan batu dai na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Najeriyar suka kubutar da wasu mutane 829 daga hannun 'yan Boko Haram, yayin da a hannu guda kuma wasu da ake kyautata zaton mayakan na Boko haram ne suka sace wasu mata 16 cikinsu har da 'yan mata guda biyu a kusa da garin Sabon Gari da ke cikin karamar hukumar Madagali a jihar Adamawan Najeriyar.