Yaki da cin hanci a taimakon raya kasa | Siyasa | DW | 20.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yaki da cin hanci a taimakon raya kasa

matsalar cin hanci na daga cikin abubuwan dake hana ruwa gudu a manufofin raya kasashe masu tasowa

Bisa al’ada dai akan kwatanta cin hanci da matakai na facaka da kudaden gwamnati da kuma amfani da su ta hanyoyin da ba su dace ba. Amma wannan fassarar ba ta dace ba. Saboda an danganta maganar da manufofi na haramci, wanda ke nufin idan ba kudi ne na sata ba, amfani da su bai haramta ba. Bugu da kari kuma wannan fassarar ta shafi jami’ai ne na gwamnati kawai kuma ta haka aka yi watsi da rawar da kamfanoni da ‘yan kasuwa ke takawa a wannan manufa. A saboda haka wannan fassara ba ta cika ba.

Wannan bayanin ya zo ne daga bakin Daniel Kaufmann darektan kula da al’amuran shugabanci na kasa da kasa a cibiyar bankin duniya kuma mai ba da shawara ga gwamnatocin kasashe da dama a manufofi na demokradiyya da raya kasa. Yayi shekaru masu yawa yana mai tafiyar da bincike akan matakan da suka cancanta wajen yakar cin hanci. Ya ce kyakkyawan matakin da zai kai ga nasara shi ne na tsaurara hukunci da tsage gaskiya da kuma shugabanci na gari a karkashin inuwar tsarin mulki na demokradiyya tsantsa. Shi kansa bankin duniya ya sha fuskantar kalubala sakamakon rancen kudin da ya saba ba wa gwamnatocin da ake zarginsu da almubazzaranci da cin hanci da kuma facaka da kudaden raya kasa. Bankin duniyar ma dai a hakika shi ne ke da alhakin dubban miliyoyi na rancen da aka yi shekaru gwammai suna kwarara zuwa aljifan mahukunta da jami’an gwamnatin kasashen da lamarin ya shafa. Amma a yanzu al’amura sun dauki wani sabon fasali, inda shi kansa bankin duniyar yake da sashensa na yaki da cin hanci tare da daukar matakai na riga kafi da wayar da kan jama’a in ji Jonathan Shapiro mai jan akalar matakan na farautar masu laifukan cin hanci na bankin duniya, wanda kuma yayi bayani yana mai cewar:

A gani na a yanzu muna kan wani mataki ne na ilimantarwa, inda muka tashi daga matsayi na mayar da martani zuwa ga daukar matakai na radin kai domin bin diddigin matsalar ta cin hanci. Bi ma’ana a yanzun duk wani shirin rayawar da ake bukatar rancen kudi a kansa sai mun yi bitarsa daki-daki tare da takwarorinmu da alhakin lamarin ya rataya wuyansu. A kan nema daga gare mu da mu tantance wasu daga cikin shirye-shiryen sannan mu ba da ra’ayinmu game da su.

A dai halin da ake ciki yanzu duk wata yarjejeniyar rancen kudi daga bankin duniyar sai an shigar da sharuddan yaki da cin hanci a cikinta, to amma duk da haka da yawa daga cikin kasashe masu tasowa da masu matsakaicin ci gaban masana’antu ba sa tabuka kome wajen yaki da matsalar ta cin hanci kamar yadda rahoton kungiyar yaki da cin hanci ta Transparency International ya nunar. Har yau akwai kasashe masu tarin yawa na Afurka da Asiya da Latin Amurka da kuma tsaffin janhuriyoyin rusasshiyar tarayyar Soviet dake ci gaba da fama da radadin matsalar ta cin hanci duk kuwa da nasarar da aka samu wajen tinkarar matsalar a ‘yan shekarun baya-bayan nan, in ji Jonathan Shapiro.