Yaki da azabtar da jamaa a duniya | Zamantakewa | DW | 26.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Yaki da azabtar da jamaa a duniya

Azabtarwa

Azabtarwa

Kimanin shekaru 20 kenan da aka gudanar da taron majalisar dunkin duniya,inda aka cimma rattaba hannu akan yarjejeniyar dakatar da azabtarwa,wanda ke zama wani nau’i ne na take hakkin bil adama.

A ranar 26 ga watan yunin 1987 aka rattaba hannu a yarjejeniyar haramta azatar da jamaa a sassa daban daban na duniya .Amma kawo yanzu akwai kasashe kimanin 51 da basu shiga wannan yarjejeniya ba,amma kasashe 144 da suka rattaba hannu a yarjejeniyar a halin yanzu an samu koma baya dangane da wannan matsala.Kamar yadda jamiin hulda da jamaa na cibiyar taimakawa wadanda aka azabtar na kasa da kasa dake Kopenhagen dinkasar Denmark,Sune Segal yayi bayani...

“Azabtarwa nada wani matsayi acikin hakkokin jamaa.Yana daga cikin nauo’in na batutuwa da suka sabawa dokar kare hakkin biladama da bazaa iya yafewa ba.Abun nufi anan shine,babu wani dalili,ko yanayi a kowane lokaci kuma a koina da aka halalta azabatarwa”

Wanmnan cibiya dake birnin Kopen hagen dai na taimakawa dukkan mutane dasu ka fuskanci kowane naui na azabtarwa daga koina ana kasashen duniya da magunguna domin sakle farfado da lafiyarsu ,kuma tana da kasashe kimanin 129,a matsayin wakilanta.

To ko ayyukan wannan cibiya na tafiya daidai ,da wakilan da ke karkashinta,musamman ma dayake akwai kimanin kasashe 144 da suka rattaba hannu a yarjejeniyar da aka rattabawa hannu shekaru 20 da suka gabata a taron yaki da azabtarwa da mdd ta gudanara Denmark? Sune Segal ya kada baki dacewa..

“a a ko kadan ba haka bane ,akwai kasashe 51 da har yanzu basu rattaba hannu a yarjejeniyar ba, amma har yanzu suma wasu kasashe da suka shiga wannan yarjejeniyar,ana cigaba da azabtar da mutane,kuma wannan shine babban batu sdake ciwa wannan hukuma tamu tuwo a kwarya”

Kungiyoyin kare hakkin jamaa na kasa da kasa kamar Amnesty International ,sun sha bayyana cewa baa cikanta kaidoji da aka cimma a taron na mdd.Kasashe da dama na cigaba da take hakokin jamaa ta hanyar azabatar dasu akan laifuffuka da dama,musamman inda ake da kundun tsarin mulki irin na Demokradiyya.

Hakan kuwa na cigaba da aukuwa ne musamman dayake cibiyar taimakawa wadanda ake azabtarwan dake da matsuguninta a Denmark bata sanar sunayen ainihin kasashen da suka fi samu da wadannan laifuffuka.

“Bama jera sunayen kasashen da muke zuwa gudanar da bincikenmmu,musamman inda aka fi azabtar da mutane.Idan aka dubu rahotanni da suka fito na baya bayannan daga kungiyoyin kare hakkin jamaa da dama,zaa ga cewa kasashe kamar Iraki na daya daga cikin misalan inda aka dade ana azabtar da mutane,kana itama Sudan,musamman a lardin Darfur dake fama da Rikici,da kuma kasa kamar pakistan”