Yaki da ayyukan ta´addanci a London | Labarai | DW | 01.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yaki da ayyukan ta´addanci a London

Wata kotu a London tace rundunar yan sandan kasar, tayi karan tsaye ga dokin hanya da kuma na lafiya. Hakan a cewar kotun shine yayi ummul aba´isin rasuwar dan kasar Brazil din nan, bisa zargin cewa dan kunar bakin wake ne. Mr Jean Charles De Menezes dan shekaru 27,ya rasa ran na sa ne , a watan yuli bayan yan sandan na London sun harbe shi aka, har sau bakwai.Hakan dai yazo ne makonni biyu, bayan harin kunar bakin wake ne da aka kai tashar jirgin kasan birnin ne, wanda ya halaka mutane 52. Bisa wannan laifin, kotun ta ci rundunar yan sandan tarar miliyoyin kudi na yuro.